12 Sai Sulemanu ya miƙa hadayun ƙonawa ga Ubangiji a kan bagaden da ya gina wa Ubangiji a gaban shirayi.
13 Sulemanu ya yi bisa ga abin da aka wajabta a yi kowace rana, bisa ga umarnin Musa a miƙa hadayu domin ranakun Asabar, da na amaryar wata, da kuma lokatan idodi uku na shekara, wato idin abinci marar yisti, da idin makonni, da na bukkoki.
14 Bisa ga ka'idar da tsohonsa Dawuda ya tsara, sai Sulemanu ya karkasa firistoci ƙungiya ƙungiya domin su yi hidima, Lawiyawa kuma bisa ga matsayinsu na yin yabo da hidima a gaban firistoci, kamar yadda aka wajabta kowace rana. Matsaran ƙofa kuma aka karkasa su ƙungiya ƙungiya bisa ga yawan ƙofofin, gama haka Dawuda, mutumin Allah, ya umarta.
15 Firistoci da Lawiyawa kuwa, ba su kauce wa umarnin sarki a kan kowane al'amari ba, ko a kan sha'anin taskoki.
16 Haka Sulemanu ya kammala aikinsa, da aka aza harsashin gina Haikalin Ubangiji, har zuwa ran da aka gama. Haka kuwa aka kammala aikin Haikalin Ubangiji.
17 Sai Sulemanu ya tafi Eziyon-geber da Elat da suke a gaɓar teku a ƙasar Edom.
18 Hiram kuwa ya aika wa Sulemanu jiragen ruwa tare da barori waɗanda suka saba da sha'ani a teku. Sai barorin tare da barorin Sulemanu, suka tafi Ofir, suka ɗauko zinariya talanti ɗari huɗu da hamsin, suka kawo wa sarki Sulemanu.