9 Amma Sulemanu bai bautar da kowa daga cikin mutanen Isra'ila ba, su ne mayaƙansa, da shugabannin yaƙi, da shugabannin karusansa, da mahayan dawakansa.
10 Manyan shugabanni na sarki Sulemanu, mutum ɗari biyu ne da hamsin waɗanda suke iko da jama'a.
11 Sulemanu kuwa ya kawo 'yar Fir'auna daga birnin Dawuda zuwa gidan da ya gina mata, gama ya ce, “Matata ba za ta zauna a gidan Dawuda, Sarkin Isra'ilawa ba, saboda duk wuraren da akwatin Ubangiji ya shiga sun tsarkaka.”
12 Sai Sulemanu ya miƙa hadayun ƙonawa ga Ubangiji a kan bagaden da ya gina wa Ubangiji a gaban shirayi.
13 Sulemanu ya yi bisa ga abin da aka wajabta a yi kowace rana, bisa ga umarnin Musa a miƙa hadayu domin ranakun Asabar, da na amaryar wata, da kuma lokatan idodi uku na shekara, wato idin abinci marar yisti, da idin makonni, da na bukkoki.
14 Bisa ga ka'idar da tsohonsa Dawuda ya tsara, sai Sulemanu ya karkasa firistoci ƙungiya ƙungiya domin su yi hidima, Lawiyawa kuma bisa ga matsayinsu na yin yabo da hidima a gaban firistoci, kamar yadda aka wajabta kowace rana. Matsaran ƙofa kuma aka karkasa su ƙungiya ƙungiya bisa ga yawan ƙofofin, gama haka Dawuda, mutumin Allah, ya umarta.
15 Firistoci da Lawiyawa kuwa, ba su kauce wa umarnin sarki a kan kowane al'amari ba, ko a kan sha'anin taskoki.