11 Ubangiji ya ce,“Mutanen Edom sun ci gaba da yinzunubi.Hakika, zan hukunta su,Don sun farauci 'yan'uwansu,Isra'ilawa,Suka ƙi su nuna musu jinƙai.Ba su yarda su huce daga fushinsuba.
12 Saboda haka zan aukar da wuta akan Teman,Ta ƙone kagarar Bozara.”
13 Ubangiji ya ce,“Mutanen Ammon sun ci gaba da yinzunubi.Hakika, zan hukunta su,Don haɗamarsu ta ƙasa,Suka tsaga mata masu ciki aGileyad.
14 Saboda haka zan aukar da wuta akan garun Rabba,Ta ƙone kagarar birnin.Za a yi kururuwa a ranar yaƙi,Faɗan kuwa zai yi rugugi kamarhadiri.