1 Ku kasa kunne ga wannan, ya kumatan Samariya,Ku da kuka yi ƙiba kamarturkakkun shanu,Ku da kuke wulakanta kasassu,Kuna yi wa matalauta danniya,Kukan umarci mazajenku,Ku ce, “Kawo mini abin sha!”
2 Da yake Ubangiji Mai Tsarki neYa riga ya yi alkawari,Ya ce, “Hakika kwanaki za su zoDa za a jawo ku da ƙugiyoyi,Kowannenku zai zama kamar kifi aƙugiya.
3 Za a kwashe ku, a fitar da kuTa inda garu ya tsage na mafi kusaduka, a jefar.”
4 Ubangiji ya ce,“Jama'ar Isra'ila,Ku tafi Betel, tsattsarkan wuri,Ku yi ta zunubi!Ku tafi Gilgal ku ƙara zunubi!Ku yi ta kawo dabbobi sadakakowace safiya.A kowace rana ta ukuKu yi ta ba da zaka.
5 Ku miƙa abincinku hadaya tagodiya.Ku yi ta yin fariya da hadayarku tayardar rai!Gama irin abin da kuke jin daɗin yike nan.”