1 Ku kasa kunne, ku jama'arIsra'ila, ga waƙar makoki da zan yia kanku.
2 Isra'ila ta fāɗi,Ba kuwa za ta ƙara tashi ba.Tana fa kwance a ƙasa,Ba wanda zai tashe ta.
3 Ubangiji ya ce,“Wani birnin Isra'ila ya aika da sojadubu,Ɗari ne kaɗai suka komo,Wani birni kuma ya aika da soja ɗarine,Amma goma kaɗai suka komo.”
4 Ubangiji ya ce wa jama'ar Isra'ila,“Ku zo gare ni, za ku tsira.
5 Kada ku tafi ku yi sujada a Biyer-sheba.Kada ku yi ƙoƙarin nemana aBetel,Gama Betel lalacewa za ta yi.Kada ku tafi Gilgal,Gama an ƙaddara wa jama'arta suyi ƙaura.”