17 Za a yi kuka ko'ina cikin dukangonakin inabinkuGama zan zo in yi muku horo.”
18 Taku ta ƙare, ku da kuke marmarinzuwan ranan nan ta Ubangiji!Wane amfani wannan rana za ta yimuku?Rana ta baƙin ciki ce,Ba ta murna ba.
19 Zai zama kamar wanda ya tsere wazakiYa fāɗa a bakin beyar!Ko kuwa kamar wanda ya komogida,Ya dāfa bango, maciji ya sare shi.
20 Ranar Ubangiji za ta kawo baƙinciki,Ba murna ba.Rana ce ta damuwa ba ta fara'a ba.
21 Ubangiji ya ce,“Na ƙi bukukuwanku na addini.Ina ƙyamarsu!
22 Sa'ad da kuka kawo mini hadayunƙonawaDa hadayunku na tsaba, ba zankarɓa ba.Ba kuma zan karɓi turkakkundabbobinkuWaɗanda kuka miƙa mini hadayungodiya ba.
23 Ku yi shiru da yawan hargowarwaƙoƙinku.Ba na so in saurari kaɗe-kaɗenku dabushe-bushenku.