3 Waƙoƙin da akan raira a fāda, za su zama na makoki a wannan rana. Za a iske gawawwaki ko'ina. Ba za a ji motsin kome ba.”
4 Ku ji wannan, ku da kuke tattake masu bukata, kuna ƙoƙari ku hallakar da matalautan ƙasar.
5 Kuna ce wa kanku, “Mun ƙosakeɓaɓɓun kwanakin nan su wuce,Mu sami damar yin kasuwancinmu.Yaushe Asabar ɗin za ta ƙare ne?Ko mā sami damar kai hatsinmukasuwa,Mu sayar musu da tsada,Mu yi awo da ma'aunin zalunci,Mu daidaita ma'auni yadda za mucuci mai saya?
6 Za mu sayi matalauci da azurfa yazama bawa,Mai fatara kuma da takalmabi-shanu.Za mu sayar da ruɓaɓɓen hatsi,Mu ci riba mai yawa.”
7 Ubangiji Allahn Isra'ila ya riga yarantse,Ya ce, “Ba zan manta da mugayenayyukanku ba.
8 Shi ya sa ƙasar za ta girgiza,Duk wanda yake cikinta zai yi baƙinciki.Ƙasa duka za ta girgiza.Za ta hau ta sauka kamar Kogin Nilu.
9 A wannan lokaci rana za ta fāɗi datsakar rana,Duniya ta duhunta da rana kata.Ni, Ubangiji ne na faɗa.