6 Za mu sayi matalauci da azurfa yazama bawa,Mai fatara kuma da takalmabi-shanu.Za mu sayar da ruɓaɓɓen hatsi,Mu ci riba mai yawa.”
7 Ubangiji Allahn Isra'ila ya riga yarantse,Ya ce, “Ba zan manta da mugayenayyukanku ba.
8 Shi ya sa ƙasar za ta girgiza,Duk wanda yake cikinta zai yi baƙinciki.Ƙasa duka za ta girgiza.Za ta hau ta sauka kamar Kogin Nilu.
9 A wannan lokaci rana za ta fāɗi datsakar rana,Duniya ta duhunta da rana kata.Ni, Ubangiji ne na faɗa.
10 Zan mai da bukukuwanku makoki,In sa waƙoƙinku na murna su zamana makoki.Zan sa muku tufafin makoki,In sa ku aske kanku.Za ku yi makoki kamar iyayen dasuka rasa tilon ɗansu.Ranan nan mai ɗaci ce har ƙarshe.
11 “Lokaci yana zuwa da zan aiko dayunwa a ƙasar.Mutane za su ji yunwa,Ba ta abinci ba,Za su ji ƙishi,Ba na ruwa ba.Za su ji yunwar rashin samun saƙodaga wurin Ubangiji.Ni Ubangiji ne, na faɗa.
12 Mutane za su raunana, su riƙa kaida kawowa,Daga gabas zuwa yamma, dagakuma kudu zuwa arewa.Za su dudduba ko'ina suna nemansaƙo daga Ubangiji,Ba kuwa za su samu ba.