1 Na ga Ubangiji na tsaye a wajen bagade. Ya yi umarni, ya ce,“Bugi ginshiƙan Haikali don shirayiduka yă girgiza.Farfasa su, su fāɗi a kan mutane!Sauran mutane kuwa,Zan kashe su a wurin yaƙi.Ba wanda zai tsere, ko ɗaya.
2 Ko da za su nutsa zuwa lahira,Zan kama su.Ko sun hau Sama,Zan turo su.
3 Ko da za su hau su ɓuya a bisaƙwanƙolin Dutsen Karmel,Zan neme su in cafko su.Ko da za su ɓuya mini a ƙarƙashinteku,Sai in sa dodon ruwa yă yayyage su.
4 Idan kuwa abokan gābansu ne sukakama su,In umarce su su hallaka su datakobi,Tun da na yi ƙudurin ƙare su.”
5 Ubangiji Allah Mai RundunaYa taɓi duniya, ta girgiza.Duk waɗanda suke zaune cikintaSuna baƙin ciki.Duniya duka takan hauTa kuma gangara kamar ruwanKogin Nilu.