5 Ubangiji Allah Mai RundunaYa taɓi duniya, ta girgiza.Duk waɗanda suke zaune cikintaSuna baƙin ciki.Duniya duka takan hauTa kuma gangara kamar ruwanKogin Nilu.
6 Ubangiji ya gina al'arshinsa a sama,Ya shimfiɗa samaniya a bisa duniya.Ya sa ruwan teku ya zo,Ya kwarara shi a bisa duniya.Sunansa Ubangiji ne!
7 Ubangiji ya ce, “Jama'ar Isra'ila,Ina yi da ku daidai yadda nake yi daHabashawa.Na fito da Filistiyawa daga Kaftor,Suriyawa kuwa daga Kir,Daidai yadda na fito da ku dagaMasar.
8 Ina dai kallon mulkin nan mai zunubi.Zan hallaka su daga duniya,Amma ba zan hallaka dukan jama'arYakubu ba.
9 “Zan umarta a rairayi jama'ar Isra'ilaDa matankaɗi kamar hatsi.Zan rairaye su daga cikin sauranal'umma,Duk da haka ko ƙwaya ɗaya ba zata salwanta ba.
10 Masu zunubi daga cikin jama'ata zasu mutu a yaƙi,Wato dukansu da suke cewa,‘Allah ba zai bar wata masifa takusace mu ba!’ ”
11 “Wata rana zan sāke tayar da birninDawudaTankar yadda akan ta da gidan da yarushe.Zan gyara garunsa, in sāke mai dashi.Zan sāke gina shi in mai da shikamar yadda yake tun dā.