3 Yana kuma fushi da abokan nan uku na Ayuba, domin sun rasa amsar da za su ba Ayuba, ko da yake sun hurta Ayuba ne yake da laifi.
4 Elihu ya jira sai a wannan lokaci ne ya yi magana da Ayuba, don shi ne yaro a cikinsu duka.
5 Sa'ad da Elihu ya ga mutanen nan uku ba su da wata amsa da za su ba Ayuba, sai ya yi fushi.
6 Elihu ɗan Barakel, mutumin Buz, ya fara magana, ya ce,“A shekaru dai ni yaro ne ku kuwa manya ne,Don haka ina jin nauyi,Ina kuma jin tsoro in faɗa muku ra'ayina.
7 Na ce wa kaina, ‘Ya kamata kwanaki su yi magana,Yawan shekaru kuma su koyar da hikima.’
8 Amma Ruhun Allah Mai Iko Dukka ne wanda yake cikin mutum,Yakan ba mutane basira.
9 Ba tsofaffi ne masu wayo ba,Ba kuma masu yawan shekaru kaɗai yake gane abin da yake daidai ba.