3 Ubangiji ya yi magana da Ezekiyel, firist, ɗan Buzi, a ƙasar Kaldiyawa, kusa da kogin Kebar. Ikon Ubangiji yana bisa kansa.
4 Da na duba, sai ga hadiri mai iska ya taso daga wajen arewa, da wani babban girgije da haske kewaye da shi, da wuta tana ta ci falfal. A tsakiyar wutar wani abu yana walƙiya kamar tagulla.
5 Daga tsakiya wutar, sai ga kamannin waɗansu talikai su huɗu. Ga irin kamanninsu, suna kama da mutane.
6 Amma kowannensu yana da fuskoki huɗu, da fikafikai huɗu.
7 Ƙafafunsu miƙaƙƙu ne, tafin sawayensu yana kama da na maraƙi, suna walƙiya kamar gogaggiyar tagulla.
8 Suna kuma da hannuwa kamar na mutane a ƙarƙarshin fikafikansu huɗu. Ga yadda fuskoki da fikafikan talikai huɗu ɗin suke.
9 Fikafikansu suna taɓa juna, kowannensu ya miƙe gaba, ba su juyawa sa'ad da suke tafiya.