1 Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,
2 “Ɗan mutum da me itacen kurangar inabi ya fi wani itace? Da me reshen kurangar inabi ya fi wani reshen itacen da yake a kurmi?
3 Za a sami itace a cikin kuranga a yi aiki da shi? Ko kuwa mutane za su iya samun maratayi a cikinta don su rataye kaya?
4 Ga shi, akan sa ta a wuta. Sa'ad da wutar ta cinye kanta da gindinta tsakiyarta kuma ta babbake, tana da amfani don yin wani aiki kuma?
5 Ga shi ma, lokacin da take cikakkiya, ba ta da wani amfani, balle bayan da wuta ta babbake ta, za a iya yin amfani da ita?
6 “Domin haka, ni Ubangiji Allah na ce, kamar itacen kurangar inabi a cikin itatuwan kurmi, wanda na sa ya zama itacen wuta, haka zan sa mazaunan Urushalima su zama.
7 Zan yi gāba da su, ko da yake sun tsere wa wuta, duk da haka wuta za ta cinye su. Za ku sani ni ne Ubangiji sa'ad da na tashi yin gāba da su.
8 Zan sa ƙasar ta zama kufai domin sun yi rashin aminci, ni Ubangiji Allah na faɗa.”