Ez 29 HAU

Annabci a kan Masar

1 A kan rana ta goma sha biyu ga watan goma a shekara ta goma, sai Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,

2 “Ɗan mutum, ka fuskanci Fir'auna Sarkin Masar, ka yi annabci gāba da shi da dukan Masar.

3 Ka yi magana, ka ce, Ubangiji Allah ya ce,‘Ga shi, ina gāba da kai, kai Fir'auna Sarkin Masar,Babban mugun dabba wanda yake kwance a tsakiyar koguna,Wanda yake cewa, Kogin Nilu naka ne, kai ka yi shi.

4 Zan sa ƙugiyoyi a muƙamuƙanka,In kuma sa kifayen kogunanka su manne a ƙamborinka,Zan jawo ka daga cikin tsakiyar kogunanka,Da dukan kifayen kogunanka, waɗanda suka manne a ƙamborinka,

5 Zan yashe ka, kai da dukan kifayen kogunanka cikin jeji.Za ka fāɗi a fili, ba kuwa wanda zai ɗauke ka, ya binne ka.Zan sa ka zama abincin namomin jeji da tsuntsayen sararin sama.

6 A sa'an nan mazaunan Masar za su sani ni ne Ubangiji,Domin sun zama wa mutanenIsra'ila kamar sandan iwa.

7 Sa'ad da suka riƙe ka,Sai ka karye ka tsattsaga hannuwansu.Sa'ad da suka jingina da kai,Sai ka karye, har ka sa kwankwasonsu ya firgiza.

8 Saboda haka, ni Ubangiji Allah na ce zan jawo takobi a kanka, in kashe mutanenka, duk da dabbobi.

9 Ƙasar Masar za ta zama kufai, marar amfani. Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji.“ ‘Domin ka ce, “Kogin Nilu nawa ne, ni na yi shi,”

10 ina gāba da kai da kogunanka. Zan mai da ƙasar Masar kufai sosai, marar amfani, tun daga Migdol zuwa Sewene har zuwa iyakar Habasha.

11 Mutum ko dabba ba zai ratsa ta cikinta ba. Za ta zama kufai har shekara arba'in.

12 Zan mai da ƙasar Masar kufai fiye da sauran ƙasashe. Biranenta za su zama kufai marar amfani, fiye da sauran birane har shekara arba'in. Zan kuma warwatsar da Masarawa a cikin sauran al'umma.’ ”

13 Ubangiji Allah ya ce, “Bayan shekara arba'in zan tattaro Masarawa daga cikin sauran al'umma inda aka warwatsar da su.

14 Zan komo da Masarawa, in maido su a ƙasar Fatros, ƙasarsu ta ainihi. Za su zama mulki marar ƙarfi.

15 Za su zama rarraunan mulki a cikin mulkoki. Ba za su ƙara ɗagawa sauran al'umma kai ba. Zan sa su zama kaɗan, har da ba za su ƙara mallakar waɗansu al'ummai ba.

16 Ba za su ƙara zama abin dogara ga mutanen Isra'ila ba, gama Isra'ilawa za su tuna da laifin suka yi, suka nemi taimakon Masarawa. Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji Allah.”

17 A kan rana ta fari ga watan fari a shekara ta ashirin da bakwai, sai Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,

18 “Ɗan mutum, Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya sa sojojinsa su matsa wa Taya. Kowane kai ya koɗe, kowace kafaɗa kuma ta yi kanta, amma duk da haka shi, tare da sojojinsa, bai sami hakkin wahalar da ya sha a Taya ba.”

19 Domin haka Ubangiji Allah ya ce, “Zan ba Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ƙasar Masar, zai kwashe dukiyarta, ya lalatar da ita, ya washe ta ganima. Za ta zama abin biyan sojojinsa.

20 Na ba shi ƙasar Masar saboda wahalar da ya sha, gama ni suka yi wa aiki. Ni Ubangiji Allah na faɗa.

21 “A ranan nan zan naɗa ɗaya daga cikin zuriyar Dawuda ya zama babban sarki, zan kuma buɗe bakinka a tsakiyarsu. Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji.”