10 Dukansu kuwa kamanninsu ɗaya, kamar ƙafa a cikin ƙafa.
11 Sa'ad da suke tafiya, sukan tafi kowane waje, ba sai sun juya ba. Duk wajen da ƙafar gaba ta nufa, nan sauran za su bi, ba sai sun juya ba.
12 Suna da idanu a jikunansu ko'ina, a bayansu, da hannuwansu, da fikafikansu da kuma ƙafafunsu.
13 Na ji ana kiran ƙafafun, ƙafafun guguwa.
14 Kowane kerub yana da fuska huɗu. Fuska ta fari ta kerub ce, fuska ta biyu ta mutum ce, fuska ta uku ta zaki ce, fuska ta huɗu kuwa ta gaggafa ce.
15 Kerubobin kuwa suka tashi sama. Waɗannan su ne talikai huɗu waɗanda na gani a bakin kogin Kebar.
16 Sa'ad da kerubobin suka tafi, ƙafafun kuma sukan tafi tare da su. Sa'ad da suka ɗaga fikafikansu don su tashi daga ƙasa zuwa sama, ƙafafun kuma ba su barinsu.