1 Sai Ruhu ya ɗaga ni sama, ya kai ni ƙofar gabas ta Haikalin Ubangiji wadda dake fuskantar gabas. Sai ga mutum ashirin da biyar a bakin ƙofar. A cikinsu na ga Yazaniya ɗan Azzur, da Felatiya ɗan Benaiya, shugabannin jama'a.
2 Sai ya ce mini, “Ɗan mutum, waɗannan su ne mutanen da suke ƙulla mugunta, waɗanda suke ba da muguwar shawara a cikin birnin.
3 Waɗanda suke cewa, ‘Lokacin gina gidaje bai yi kusa ba. Wannan birni tukunya ce mai ɓararraka, mu ne kuwa naman.’
4 Saboda haka ka yi musu annabci marar kyau, ka yi annabci, ya ɗan mutum!”
5 Sa'an nan Ruhun Ubangiji ya sauko a kaina, ya ce mini, “Ka ce, ‘In ji Ubangiji, haka kuke tunani, ku mutanen Isra'ila, gama na san abin da yake cikin zuciyarku.
6 Kun kashe mutane da yawa a wannan birni, har kun cika titunansa da gawawwaki.’
7 “Domin haka Ubangiji Allah ya ce, ‘Gawawwakin da kuka shimfiɗa a cikin birnin su ne naman, birnin kuwa shi ne tukunya mai ɓararraka, amma za a fitar da ku daga cikinsa.