6 Kun kashe mutane da yawa a wannan birni, har kun cika titunansa da gawawwaki.’
7 “Domin haka Ubangiji Allah ya ce, ‘Gawawwakin da kuka shimfiɗa a cikin birnin su ne naman, birnin kuwa shi ne tukunya mai ɓararraka, amma za a fitar da ku daga cikinsa.
8 Kun tsorata saboda takobi, ni kuwa zan kawo muku takobi,’ in ji Ubangiji Allah.
9 ‘Zan fitar da ku daga cikin birnin, in bashe ku a hannun baƙi, zan hukunta ku.
10 Za a kashe ku da takobi. Zan hukunta ku duk inda kuke a Isra'ila, sa'an nan za ku sani ni ne Ubangiji.
11 Birnin ba zai zama muku tukunya mai ɓararraka ba, ba kuwa za ku zama nama a cikinsa ba. Zan hukunta ku duk inda kuke a Isra'ila.
12 Za ku kuwa sani ni ne Ubangiji, gama ba ku kiyaye dokokina da ka'idodina ba, amma kuka kiyaye ka'idodin sauran al'umma waɗanda suke kewaye da ku.”’