8 Kun tsorata saboda takobi, ni kuwa zan kawo muku takobi,’ in ji Ubangiji Allah.
9 ‘Zan fitar da ku daga cikin birnin, in bashe ku a hannun baƙi, zan hukunta ku.
10 Za a kashe ku da takobi. Zan hukunta ku duk inda kuke a Isra'ila, sa'an nan za ku sani ni ne Ubangiji.
11 Birnin ba zai zama muku tukunya mai ɓararraka ba, ba kuwa za ku zama nama a cikinsa ba. Zan hukunta ku duk inda kuke a Isra'ila.
12 Za ku kuwa sani ni ne Ubangiji, gama ba ku kiyaye dokokina da ka'idodina ba, amma kuka kiyaye ka'idodin sauran al'umma waɗanda suke kewaye da ku.”’
13 Sa'ad da nake yin annabci, sai Felatiya ɗan Benaiya, ya rasu. Sai na faɗi rubda ciki na fashe da kuka, na ce, “Ya Ubangiji Allah, za ka ƙare sauran mutanen Isra'ila ƙaƙaf ne?”
14 Ubangiji kuwa ya yi magana da ni, ya ce,