1 Sai Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,
2 “Ya ɗan mutum, ka yi annabci a kan annabawan Isra'ila. Ka yi annabci a kan waɗanda suke annabci bisa ga ra'ayin kansu, ka ce, ‘Ku ji maganar Ubangiji!’
3 “Ubangiji Allah ya ce kaito ga wawayen annabawa waɗanda suke bin ra'ayin zuciyarsu, ba su kuwa ga wani wahayi ba.
4 Ya Isra'ila, annabawanki suna kamar diloli a kufai.