5 Ba ku ƙaura zuwa inda garu ya tsage ba, ba ku gina wa mutanen Isra'ila garu don su kāre kansu a lokacin yaƙi, a ranar Ubangiji ba.
6 Suna faɗar ƙarya, suna kuma yin duban ƙarya, suna cewa, ‘Ubangiji ya ce,’ alhali kuwa Ubangiji bai aike su ba, duk da haka sun sa zuciya ga cikawar maganarsu.
7 Wahayin ƙarya ne kuka gani, kuna yin duban ƙarya, sa'ad da kuke cewa, ‘Ubangiji ya faɗa,’ ko da yake ni Ubangiji ban faɗa ba.
8 “Saboda haka ni Ubangiji Allah na ce, da yake kun yi maganar wofi, kun ga wahayin ƙarya, ina gāba da ku.
9 Ikona zai yi gāba da annabawan da suke ganin wahayin ƙarya, waɗanda suke kuma yin duban ƙarya. Ba za su kasance cikin taron mutanena ba, ba kuwa za a rubuta su a littafin mutanen Isra'ila ba, ba za su shiga ƙasar Isra'ila ba. Za ku kuwa sani, ni ne Ubangiji Allah.
10 “Domin sun ɓad da mutanena suna cewa, ‘Salama,’ sa'ad da ba salama, sa'ad da kuma mutanen suke gina garu marar aminci, sai annabawan nan su shafe shi da farar ƙasa,
11 ka faɗa wa waɗanda suka shafe garun da farar ƙasa, cewa zai faɗi. Za a yi rigyawa da ƙanƙara, da babban hadiri mai iska.