1 Waɗansu dattawa na Isra'ila suka zo wurina, suka zauna a gabana.
2 Sai Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,
3 “Ɗan mutum, waɗannan mutane sun sa zukatansu ga bin gumaka, sun sa abin tuntuɓe a gabansu, zan fa yarda su yi tambaya a wurina?
4 “Sai ka faɗa musu, cewa Ubangiji Allah ya ce duk mutumin Isra'ila, wanda ya manne wa gumaka, ya sa abin tuntuɓe a gabansa sa'an nan kuma ya zo wurin annabi, ni Ubangiji zan sāka masa gwargwadon yawan gumakansa,
5 domin in kama zukatan mutanen Isra'ila waɗanda suka zama baƙi a gare ni, saboda gumakansu.
6 “Domin haka ka ce wa mutanen Isra'ila, ‘Ubangiji ya ce ku tuba, ku rabu da gumakanku, da abubuwanku na banƙyama.
7 “‘Gama duk wanda yake na Isra'ila da dukan baƙin da suke baƙunta cikin Isra'ila, wanda ya rabu da ni, ya manne wa gumakansa, ya sa abin tuntuɓe a gabansa, sa'an nan ya zo yana roƙona a wurin annabi, ni Ubangiji zan sāka masa.