1 Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce,
2 “Ɗan mutum, ka sa Urushalima ta san ayyukanta na banƙyama.
3 Ka faɗa wa Urushalima abin da ni Ubangiji Allah na ce mata.”Ubangiji ya ce, “Asalinki da haihuwarki daga ƙasar Kan'ana ne. Mahaifinki Ba'amore ne, mahaifiyarki kuwa Bahittiya ce.
4 Game da haihuwarki kuwa, ran da aka haife ki, ba a yanke cibiyarki ba, ba a kuma yi miki wanka da ruwa don a tsabtace ki ba, ba a kuma goge ki da gishiri ba, ba a naɗe ki cikin tsummoki ba.