45 Ke 'yar mahaifiyarki ce wadda ta ƙi mijinta da 'ya'yanta. Ke kuma 'yar'uwar 'yar'uwanki mata ce waɗanda suka ƙi mazansu da 'ya'yansu. Mahaifiyarki Bahittiya ce, mahaifinki kuwa Ba'amore ne.
46 “'Yarki ita ce Samariya wadda take zaune da 'ya'yanta mata wajen arewa da yake. Ƙanwarki ita ce Saduma wadda take zaune kudu da ke tare da 'ya'yanta mata.
47 Ba ki bi hanyoyinsu da abubuwansu na banƙyama kaɗai ba, sai ka ce wannan ya yi miki kaɗan, amma kin lalace fiye da su.
48 “Hakika ni Ubangiji Allah na ce Saduma ƙanwarki da 'ya'yanta mata ba su yi kamar yadda ke da 'ya'yanki mata kuka yi ba.
49 Wannan shi ne laifin Saduma, ƙanwarki, ita da 'ya'yanta mata, suna da girmankai domin suna da abinci a wadace, suna zama a sangarce, amma ba su taimaki matalauta da masu bukata ba.
50 Su masu alfarma ne, sun aikata abubuwa masu banƙyama a gabana, saboda haka na kawar da su sa'ad da na gani.
51 “Samariya ba ta aikata rabin zunubin da kika aikata ba. Abubuwan banƙyama da kika aikata sun sa 'yan'uwanki sun zama kamar adalai.