47 Ba ki bi hanyoyinsu da abubuwansu na banƙyama kaɗai ba, sai ka ce wannan ya yi miki kaɗan, amma kin lalace fiye da su.
48 “Hakika ni Ubangiji Allah na ce Saduma ƙanwarki da 'ya'yanta mata ba su yi kamar yadda ke da 'ya'yanki mata kuka yi ba.
49 Wannan shi ne laifin Saduma, ƙanwarki, ita da 'ya'yanta mata, suna da girmankai domin suna da abinci a wadace, suna zama a sangarce, amma ba su taimaki matalauta da masu bukata ba.
50 Su masu alfarma ne, sun aikata abubuwa masu banƙyama a gabana, saboda haka na kawar da su sa'ad da na gani.
51 “Samariya ba ta aikata rabin zunubin da kika aikata ba. Abubuwan banƙyama da kika aikata sun sa 'yan'uwanki sun zama kamar adalai.
52 Ke kuma sai ki sha kunyarki, gama kin sa 'yan'uwanki mata su sami rangwamin shari'a saboda zunubanki da kika aikata fiye da nasu, gama gwamma su da ke. Sai ki ji kunya, ki sha ƙasƙancinki, gama kin sa 'yan'uwanki mata su zama kamar adalai.”
53 Ubangiji ya ce wa Urushalima, “Zan komo da Saduma da Samariya da 'ya'yansu mata daga bauta. Sa'an nan zan komo da ke daga bauta tare da su,