1 Sai ya ce mini, “Ɗan mutum, ka tashi tsaye, zan yi magana da kai.”
2 Da ya yi magana da ni, sai Ruhu ya sauko a kaina, ya ta da ni tsaye, sa'an nan na ji yana magana da ni.
3 Ya ce mini, “Ɗan mutum na aike ka zuwa wurin jama'ar Isra'ila, al'umma mai tayarwa, waɗanda suka tayar mini. Su da ubanninsu suna yi ta yi mini laifi har yau.
4 Su mutane ne marasa kunya, masu taurinkai. Ga shi kuwa, na aike ka gare su, ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Runduna ya faɗa.’
5 Ko su ji, ko kada su ji, gama su masu tayarwa ne, amma za su sani akwai annabi a cikinsu.