5 Ko su ji, ko kada su ji, gama su masu tayarwa ne, amma za su sani akwai annabi a cikinsu.
6 “Kai ɗan mutum, kada ka ji tsoronsu, kada kuma ka ji tsoron maganganunsu, ko da ya ke ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya sun kewaye ka, kana kuma zaune tare da kunamai. Kada ka ji tsoron maganganunsu ko ka karai saboda irin kallon da za su yi maka, gama su 'yan tawaye ne.
7 Za ka faɗa musu maganata, ko su ji, ko kada su ji, gama su 'yan tawaye ne.
8 “Amma kai, ya ɗan mutum, ka ji abin da zan faɗa maka, kada ka zama mai tayarwa kamar 'yan tawayen nan. Sai ka buɗe bakinka, ka ci abin da zan ba ka.”
9 Da na duba, sai ga hannu yana miƙo mini littafi.
10 Ya buɗe littafin a gabana, akwai rubutu ciki da baya. Ba abin da aka rubuta sai maganganun baƙin ciki, da makoki, da kaito.