1 A kan rana ta goma ga watan biyar a shekara ta bakwai, sai waɗansu dattawan Isra'ila suka zo don su yi roƙo a wurin Ubangiji. Suka zauna a gabana.
2 Ubangiji kuwa ya yi magana da ni ya ce,
3 “Ɗan mutum, ka faɗa wa dattawan Isra'ila cewa, ‘Ni Ubangiji Allah na ce kun zo ku yi roƙo a wurina, amma hakika, ba na roƙuwa a gare ku.’
4 “Za ka shara'anta su? Ɗan mutum, shara'anta su. To, sai ka sanar da su abubuwa masu banƙyama waɗanda kakanninsu suka yi.