32 Tunanin nan da kuke yi a zuciyarku, cewa kuna so ku zama kamar sauran al'umma da kabilan ƙasashe, ku bauta wa itace da dutse, ba zai taɓa faruwa ba.’
33 “Hakika, ni Ubangiji Allah na ce, zan sarauce ku ƙarfi da yaji, da fushi,
34 da ƙarfi da yaji da fushi kuma, zan fito da ku daga cikin mutane, in tattaro ku daga sauran ƙasashe inda aka warwatsa ku.
35 Zan kawo ku cikin ruƙuƙin jama'a, in yi muku shari'a fuska da fuska.
36 Kamar yadda na yi wa kakanninku shari'a a jejin ƙasar Masar, haka kuma zan yi muku shari'a, ni Ubangiji Allah na faɗa.
37 “Zan sa ku wuce ta ƙarƙashin sanda, in ƙulla alkawarina da ku.
38 Zan fitar da 'yan tawaye a cikinku, da waɗanda suke yin mini laifi. Zan fito da su daga ƙasar da suke zaune, amma ba za su shiga ƙasar Isra'ila ba. Za ku kuwa sani ni ne Ubangiji Allah.