8 Amma suka tayar mini, ba su ji ni ba, ba su yi watsi da abubuwan banƙyama da suke jin daɗinsu ba, ba su rabu da gumakan Masarawa ba. Sai na ce zan zubo musu da hasalata, in aukar musu da fushina a ƙasar Masar.
9 Amma saboda sunana ban yi wannan ba, domin kada a saɓi sunana cikin sauran al'umma inda mutanen Isra'ila suke zaune, gama na sanar da kaina ga mutanen Isra'ila, a gaban sauran al'umma kuma, sa'ad da na fito da mutanen Isra'ila, daga ƙasar Masar.
10 “Sai na fisshe su daga ƙasar Masar, na kawo su cikin jeji.
11 Na ba su dokokina da ka'idodina, waɗanda idan mutum ya kiyaye su, zai rayu.
12 Na kuma ba su ranar Asabar don ta zama alama tsakanina da su, don kuma su sani ni ne Ubangiji wanda yake tsarkake su.
13 Amma mutanen Isra'ila suka tayar mini a cikin jeji, ba su bi dokokina da ka'idodina ba, waɗanda idan mutum ya kiyaye su, zai rayu. Suka ɓata ranar Asabar ƙwarai. Sai na ce zan zubo musu da hasalata, in aukar da fushina a kansu.
14 Amma saboda sunana ban yi wannan ba, domin kada a saɓi sunana a cikin sauran al'umma waɗanda a kan idonsu na fisshe su.