1 Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce,
2 “Kai ɗan mutum, za ka shara'anta? Za ka shara'anta birni mai kisankai? To, sai ka faɗa masa dukan ayyukansa na banƙyama.
3 Sai ka ce masa, ‘Ni Ubangiji Allah na ce, birnin da yake kisankai, yana kuma bauta wa gumaka don ya ƙazantar da kansa, lokacinsa zai yi!
4 Ka yi laifi saboda ka zubar da jini, ka ƙazantar da kanka da gumakan da ka yi. Saboda haka ka matso da lokacinka kusa, ƙayyadaddun shekarunka sun cika. Domin haka na maishe ka abin zargi ga sauran al'umma, da abin ba'a ga dukan ƙasashe.