10 Waɗannan suka tsiraita ta, suka kama 'ya'yanta mata da maza, suka kashe ta da takobi. Sai ta zama abin karin magana a wurin mata sa'ad da aka hukunta ta.
11 “Ƙanwarta kuwa ta ga wannan, amma duk da haka ta fi ta lalacewa saboda kai da kawowa na karuwanci, wanda ya fi na 'yar uwarta muni.
12 Ta yi ta kai da kawowa cikin Assuriyawa, a wurin masu mulki da manyan sojoji waɗanda suke saye da kayan yaƙi, suna bisa kan dawakai, dukansu samari ne masu bansha'awa.
13 Na ga ta ƙazantu. Dukansu biyu suka bi hanya ɗaya.
14 “Amma karuwancinta ya zarce. Ta ga an zāna mutane a jikin bango, siffofin Kaldiyawa ne aka zāna da jan launi!
15 Sun sha ɗamara a gindinsu, da rawuna a kansu suna kaɗawa filfil. Dukansu suna kama da jarumawa. Su siffofi suna kama da mutanen Babila na ƙasar Kaldiya.
16 Sa'ad da ta gan su, sai ta yi ta kai da kawowa a cikinsu. Ta aiki jakadu a wurinsu, wato a Kaldiya.