15 Sun sha ɗamara a gindinsu, da rawuna a kansu suna kaɗawa filfil. Dukansu suna kama da jarumawa. Su siffofi suna kama da mutanen Babila na ƙasar Kaldiya.
16 Sa'ad da ta gan su, sai ta yi ta kai da kawowa a cikinsu. Ta aiki jakadu a wurinsu, wato a Kaldiya.
17 Sai Babilawa suka zo wurinta, a gadonta na nishaɗi, suka ƙazantar da ita ta wurin kwana da ita. Bayan da sun ƙazantar da ita, sai ta ji ƙyamarsu, ta rabu da su.
18 Ta yi ta karuwancinta a fili, ta bayyana tsiraicinta. Sai na ji ƙyamarta, na rabu da ita kamar yadda na rabu da 'yar'uwarta.
19 Duk da haka ta yi ta ƙara karuwancinta, tana tunawa da kwanakin 'yan matancinta, a lokacin da ta yi karuwancinta a ƙasar Masar.
20 Ta yi ta kai da kawowa tsakanin kwartayenta waɗanda al'auransu kamar na jakai ne, maniyyinsu kuwa kamar na dawakai ne.
21 Haka kika yi ƙawar zucin lalatar da kika yi a lokacin 'yan matancinki, sa'ad da Masarawa suka rungumi mamanki na ƙuruciya.”