1 A kan rana ta goma ga watan goma, a shekara ta tara, sai Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,
2 “Ɗan mutum, ka rubuta sunan wannan rana. Ranar ke nan da Sarkin Babila ya kewaye Urushalima da yaƙi.
3 Ka yi wa 'yan tawayen nan magana da misali, ka faɗa musu cewa, ni Ubangiji na ce,‘Ka ɗora tukunya, ka ɗora ta a wuta,Ka cika ta da ruwa.
4 Ka zuba gunduwoyin nama a ciki,Dukan gunduwoyi masu kyau, wato cinya da kafaɗa,Ka cika ta da tantakwashi.
5 Ka kama mafi kyau daga cikin garken,Ka sa sauran ƙasusuwa a ƙarƙashinsa,Ka tafasa gunduwoyin,Ka kuma tafasa tantakwashin.’