1 Ubangiji ya yi magana da ni ya ce,
2 “Dan mutum, ka faɗa wa Sarkin Taya, cewa Ubangiji Allah ya ce,‘Da yake zuciyarka ta cika da alfarma,Har ka ce kai allah ne,Kana zaune a mazaunin allah, kana zaune a tsakiyar tekuna,To, kai mutum ne kawai, ba allah ba,Ko da yake ka aza kanka mai hikima ne kamar Allah.
3 Lalle ka fi Daniyel hikima,Ba asirin da yake ɓoye a gare ka.
4 Ta wurin hikimarka da ganewarka ka samo wa kanka dukiya,Ka tattara zinariya da azurfa a baitulmalinka.