1 Sai ya ce mini, “Ɗan mutum ka ci abin da aka ba ka. Ka ci wannan littafi, sa'an nan ka tafi ka yi wa mutanen Isra'ila magana.”
2 Sai na buɗe bakina, sa'an nan ya ba ni littafin in ci.
3 Ya kuma ce mini, “Ɗan mutum, ka ci littafin nan da na ba ka, ka cika tumbinka da shi.” Sai na ci littafin, na ji shi a bakina da zaƙi kamar zuma.
4 Ya kuma ce mini, “Ɗan mutum ka tafi wurin mutanen Isra'ila ka faɗa musu maganata.
5 Gama ba a aike ka a wurin mutane waɗanda suke da baƙon harshe wanda ba ka sani ba, amma zuwa mutanen Isra'ila,
6 ba wurin waɗansu mutane dabam waɗanda suke da baƙon harshe mai wuya ba, wato harshen da ba ka sani ba. Da na aike ka wurin irin mutanen nan da za su ji.