17 Samarin Awen da na Fi-besetZa a kashe su da takobi,Matan kuma za su tafi bauta.
18 A Tafanes rana za ta yi duhu,Sa'ad da na karya mulkin ƙasar Masar,Ƙarfinta da take fariya da shi zai ƙare,Za a rufe ta da gizagizai.'Ya'yanta mata kuwa za a kai su bauta.
19 Ta haka zan hukunta Masar,Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji.”
20 A kan rana ta bakwai ga watan fari, a shekara ta goma sha ɗaya, sai Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,
21 “Ɗan mutum, na karya hannun Fir'auna, Sarkin Masar, ga shi, ba za a ɗora hannun ba, don kada ya warke ya zama da ƙarfi yadda zai iya riƙon takobi.”
22 Ubangiji Allah kuma ya ce, “Ina gāba da Fir'auna, Sarkin Masar, zan karya hannuwansa duka biyu, da lafiyayyen da kuma wanda na riga na karya. Zan sa takobinsa ya faɗi daga hannunsa.
23 Zan watsar da Masarawa a cikin sauran al'umma, in kuma warwatsa su a ƙasashen duniya.