8 Ko itatuwan al'ul da suke cikin gonar Allah, ba su kai kyansa ba.Itatuwan kasharina kuma ba su kai rassansa ba.Itatuwan durumi kuma ba su kai rassansa ba.Ba wani itace a gonar Allah wanda ya kai kyansa.
9 Na sa shi ya yi kyau, ga kuma rassansa da yawa.Dukan itatuwan Aidan, waɗanda suke cikin gonar Allah sun yi ta jin ƙyashinsa.’
10 Domin haka Ubangiji Allah ya ce, “Saboda ya yi tsayi, kansa kuma ya kai cikin gizagizai, zuciyarsa kuwa ta yi fariya saboda tsayinsa,
11 zan bashe shi a hannun mai ƙarfi, a cikin al'ummai. Zai sāka masa gwargwadon muguntarsa. Na fitar da shi.
12 Baƙi mafi bantsoro daga cikin al'ummai sun sare shi, sun bar shi. Rassansa sun faɗi a kan duwatsun da suke cikin dukan kwaruruka, rassansa kuma sun kakkarye, sun faɗi a cikin dukan magudanan ruwa na ƙasa. Dukan mutanen duniya sun tashi daga inuwarsa, sun bar shi.
13 Dukan tsuntsayen sararin sama za su zauna a gorarsa. Namomin jeji kuma za su yi ta yawo a cikin rassansa.
14 An yi wannan domin kada itatuwan da suke bakin ruwa su yi girma, su yi tsayi da yawa har kawunansu su kai cikin gizagizai, domin kuma kada itacen da yake shan ruwa ya yi tsayi kamarsa, gama an bashe su ga mutuwa zuwa lahira, tare da 'yan adam masu gangarawa zuwa cikin kabari.”