12 “Ɗan mutum, sai kuma ka faɗa wa mutanenka, cewa adalcin adali ba zai cece shi ba sa'ad da ya yi laifi, muguntar mugu kuma ba za ta sa ya mutu ba idan ya bar muguntarsa. Adalcin adali ba zai cece shi ba, idan ya shiga aikata zunubi.
13 Idan na ce wa adali, ba shakka zai rayu, amma idan ya dogara ga adalcin da ya riga ya yi, sa'an nan ya shiga aikata laifi, ba za a tuna da ayyukan adalcinsa na dā ba. Zai mutu saboda laifin da ya yi.
14 Idan kuma na ce wa mugu ba shakka zai mutu, amma idan ya bar laifinsa, ya shiga aikata adalci,
15 idan kuma ya mayar da jingina, ya mayar da abin da ya ƙwace, sa'an nan ya kiyaye dokokin rai, ya daina yin laifi, hakika, zai rayu, ba zai mutu ba.
16 Ba za a tuna da laifofin da ya aikata a dā ba, gama ya aikata adalci da gaskiya, zai rayu.
17 “Amma mutanenka sun ce, ‘Hanyar Ubangiji ba daidai ba ce,’ alhali kuwa tasu ce ba daidai ba.
18 Sa'ad da adali ya daina aikata adalci, ya shiga aikata laifi, zai mutu saboda laifinsa.