10 Ga shi, ina gāba da ku, zan nemi tumakina a hannunku. Zan hana ku yin kiwon tumakin, ku kuma ba za ku ƙara yin kiwon kanku ba. Zan ƙwace tumakina daga hannunku, domin kada su ƙara zama abincinku.”’
11 “Ni Ubangiji Allah na ce, ni kaina zan nemi tumakina.
12 Kamar yadda makiyayi yakan nemo tumakin da suka watse daga cikin garkensa, haka zan nemi tumakina. Zan cece su daga dukan wuraren da aka watsar da su a ranar gizagizai da baƙin duhu.
13 Zan fito da su daga cikin sauran al'umma, in tattaro su daga ƙasashe dabam dabam, in kawo su ƙasarsu, in yi kiwonsu a kan tuddan Isra'ila, kusa da maɓuɓɓugai, da cikin dukan wuraren da mutane suke zaune a ƙasar.
14 Zan yi kiwonsu a makiyaya mai kyau. Ƙwanƙolin tuddan Isra'ila zai zama wurin kiwonsu. Za su kwanta a makiyaya mai kyau, za su yi kiwo a makiyaya mai dausayi a kan tuddan Isra'ila.
15 Ni kaina zan yi kiwon tumakin, in ba su hutawa, ni Ubangiji Allah na faɗa.
16 “Zan nemo ɓatattu, in komo da waɗanda suka yi makuwa, in ɗora karyayyu, in ƙarfafa marasa ƙarfi, amma zan hallaka ƙarfafan makiyayan nan masu taiɓa, zan hukunta su.