34 Ƙasar da take kufai a dā za ku kafce ta maimakon yadda take kufai a kan idon dukan masu wucewa.
35 Za su ce, ‘Wannan ƙasa wadda take kufai a dā ta zama kamar gonar Aidan, ga kuma rusassun wuraren da suka zama kufai, da rusassun birane, yanzu ana zaune a cikinsu, an kuma gina musu garu.’
36 Sa'an nan al'umman da suka ragu kewaye da ku za su sani, ni Ubangiji na sāke gina rusassun wuraren da suka zama kufai. Ni Ubangiji na faɗa, zan kuwa aikata.”
37 Ubangiji Allah ya ce, “Ga abin da zan sa mutanen Isra'ila su roƙe ni, in yi musu. Za su roƙe ni in yawaita su kamar garken tumaki.
38 Kamar garken tumaki na hadaya, kamar garken tumaki a Urushalima a lokacin ƙayyadaddun idodi, haka rusassun birane za su cika da ɗumbun mutane. Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji.”