6 “Domin haka ka yi wa ƙasar Isra'ila annabci, ka ce wa duwatsu, da tuddai, da kwazazzabai, da kwaruruka, ni Ubangiji Allah na ce, ‘Ga shi, na yi magana da kishina da hasalata saboda sun sha zargi wurin al'ummai.’
7 “Domin haka ni Ubangiji Allah na rantse, cewa al'umman da suke kewaye da ku su ma za su sha zargi.
8 Amma ku, ya duwatsun Isra'ila, za ku miƙa rassanku ku ba da amfani ga mutanen Isra'ila, gama za su komo gida ba da jimawa ba.
9 Ga shi, ni naku ne, zan juyo wurinku. Za a kafce ku, a yi shuka!
10 Zan sa dukan mutanen Isra'ila su riɓaɓɓanya a cikinku. Za su zauna cikin biranen, su gina rusassun wurare.
11 Zan sa mutum da dabba su yawaita a cikinku, su kuma ba da amfani. Zan sa a zauna a cikinku kamar dā, sa'an nan zan nuna muku alheri fiye da dā. Daga nan za ku sani, ni ne Ubangiji.
12 Zan kuma sa mutanena, Isra'ila, su yi tafiya a kanku, za ku zama gādonsu, ba za ku ƙara kashe 'ya'yansu ba.