1 “Ya kai ɗan mutum, sai ka ɗauki tubali, ka ajiye a gabanka, sa'an nan ka zāna birni a kansa, wato Urushalima.
2 Sa'an nan ka gina mata kagara, da garu da ɗan tudu. Ka kuma kafa mata sansani ka kewaye ta da dundurusai.
3 Ka ɗauki kwano, ka shirya shi kamar garun ƙarfe tsakaninka da birnin, sa'an nan ka zuba ido. Birnin zai zama kamar an kewaye shi da yaƙi, kai kuwa ka kewaye shi da yaƙi. Wannan kuma zai zama alama ga Isra'ilawa.
4 “Sai kuma ka kwanta a hagunka, ni kuwa zan ɗora maka muguntar Isra'ilawa. Za ka ɗauki muguntarsu bisa ga yawan kwanakin da za ka kwanta a hagunka.