15 Tsayin murhun bagaden zai zama kamu huɗu. A kan murhun akwai zanko guda huɗu sun miƙe sama, tsawonsu kamu guda ne.
16 Murhun bagaden zai zama murabba'i ne, wato tsawonsa kamu goma sha biyu, faɗinsa kuma kamu goma sha biyu.
17 Mahaɗin kuma zai zama kamu goma sha huɗu, murabba'i. Faɗin da'irarsa zai zama rabin kamu, kewayen gindinsa zai zama kamu ɗaya. Matakan bagaden za su fuskanci gabas.”
18 Sai ya ce mini, “Ɗan mutum, ni Ubangiji Allah, na ce waɗannan su ne ka'idodin bagaden. A ranar da za a kafa shi don miƙa hadayun ƙonawa da yayyafa jini a kansa,
19 sai ka ba firistoci na zuriyar Zadok, masu yi mini hidima, bijimai na yin hadaya domin zunubi.
20 Za ka ɗibi jininsa, ka shafa shi a kan zankaye huɗu na bagaden, da kan kusurwa huɗu na mahaɗin da kan da'irarsa. Ta haka za ka tsarkake bagaden, ka yi kafara dominsa.
21 Za ka kuma ɗauki bijimi na yin hadaya domin zunubi, ka kai shi waje, a wurin da aka shirya a bayan Haikalin, ka ƙone shi.