9 Ubangiji Allah ya ce, “Ba wani baƙo marar imani da marar kaciya, daga cikin dukan baƙin da suke cikin jama'ata Isra'ila da zai shiga wurina mai tsarki.
10 “Amma Lawiyawa waɗanda suka yi nisa da ni, suka rabu da ni, suna bin gumakansu, sa'ad da mutanen Isra'ila suka karkata, za su ɗauki alhakin muguntarsu.
11 Za su zama masu hidima a cikin wurina mai tsarki, suna lura da ƙofofin Haikali, suna hidima a cikin Haikalin. Za su yanka hadayar ƙonawa da ta sadaka domin mutane. Za su lura da mutanen, su yi musu hidima.
12 Da yake sun hidimta wa mutane a gaban gumakansu, suka zama sanadin mugun tuntuɓe ga mutanen Isra'ila, don haka ni Ubangiji Allah, na yi rantsuwa cewa za su karɓi hakkin muguntarsu.
13 Ba za su zo kusa da ni a matsayin firistoci don su yi mini hidima ba. Ba za su zo kusa da abubuwana masu tsarki ba, amma za su sha kunya saboda ayyukansu na banƙyama.
14 Amma duk da haka zan sa su lura da Haikalin, su yi dukan hidimomin da za a yi a cikinsa.
15 “Amma Lawiyawan da suke firistoci daga zuriyar Zadok, waɗanda suka lura da Wuri Mai Tsarki sa'ad da mutanen Isra'ila suka karkace, suka bar bina, su ne za su zo kusa da ni, su yi mini hidima, za su kusace ni domin su miƙa hadaya ta kitse da jini, ni Ubangiji Allah na faɗa.