10 Sa'ad da suka shiga, sai sarki ya shiga tare da su, sa'ad da suka fita kuma, sai ya fita.
11 A lokacin idodi da ƙayyadaddun lokatai, gārin hadayar da za a yi tare da bijimi wajen garwa guda ne, haka kuma na wadda za a yi tare da ragon, na wadda za a yi tare da 'yan ragunan kuwa, sai mutum ya kawo gwargwadon ƙarfinsa. A kuma kawo wajen kwalaba shida na man zaitun domin kowace garwa ta gari.
12 “Sa'ad da sarki ya kawo hadayar ƙonawa ko hadayar salama ta yardar rai ga Ubangiji, sai a buɗe masa ƙofar da take fuskantar gabas. Zai kuwa miƙa hadayarsa ta ƙonawa ko ta salama kamar yadda yakan yi a ranar Asabar. Bayan da ya fita, sai a rufe ƙofa.
13 “Kowace safiya za a yi hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji da ɗan rago bana ɗaya marar lahani.
14 Tare da hadaya ta ƙonawa, za a ba da wajen ɗaya bisa shida na garwar gari, da kwalaba biyu na man zaitun don cuɗa gari, domin a yi hadaya ga Ubangiji. Wannan ita ce ka'idar hadaya ta ƙonawa ta yau da kullum.
15 Za a ba da ɗan rago, da gari, da mai, kowace safiya domin yin hadaya ta ƙonawa.
16 “Ni Ubangiji Allah na ce, idan sarki ya yi wa wani daga cikin 'ya'yansa kyauta daga cikin gādonsa, sai kyautar ta zama ta 'ya'yansa, dukiyarsu ce ta gādo.