12 “Sa'ad da sarki ya kawo hadayar ƙonawa ko hadayar salama ta yardar rai ga Ubangiji, sai a buɗe masa ƙofar da take fuskantar gabas. Zai kuwa miƙa hadayarsa ta ƙonawa ko ta salama kamar yadda yakan yi a ranar Asabar. Bayan da ya fita, sai a rufe ƙofa.
13 “Kowace safiya za a yi hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji da ɗan rago bana ɗaya marar lahani.
14 Tare da hadaya ta ƙonawa, za a ba da wajen ɗaya bisa shida na garwar gari, da kwalaba biyu na man zaitun don cuɗa gari, domin a yi hadaya ga Ubangiji. Wannan ita ce ka'idar hadaya ta ƙonawa ta yau da kullum.
15 Za a ba da ɗan rago, da gari, da mai, kowace safiya domin yin hadaya ta ƙonawa.
16 “Ni Ubangiji Allah na ce, idan sarki ya yi wa wani daga cikin 'ya'yansa kyauta daga cikin gādonsa, sai kyautar ta zama ta 'ya'yansa, dukiyarsu ce ta gādo.
17 Amma idan sarki ya yi wa wani daga cikin barorinsa kyauta daga cikin gādonsa, kyautar za ta zama tasa har shekarar 'yantarwa, sa'an nan kyautar za ta koma a hannun sarki. 'Ya'yansa maza ne kaɗai za su riƙe kyauta daga cikin gādonsa din din din.
18 Kada sarki ya ƙwace rabon gādon jama'a, ya hana musu. Sai ya ba 'ya'yansa maza rabon gādo daga cikin abin da yake nasa, amma kada ya ƙwace wa jama'ata abin da suka mallaka har su warwatse.”