5 Gārin hadaya da za a yi tare da rago wajen garwa guda ne. Wanda za a yi tare da 'yan raguna kuwa zai zama gwargwadon ƙarfinsa. Zai ba da mai wajen kwalaba shida domin kowace garwa ta gari.
6 A amaryar wata kuwa zai miƙa bijimi, da 'yan raguna shida, da rago, dukansu marasa lahani.
7 Gārin hadayar da za a yi tare da bijimin wajen garwa guda ne, haka kuma gari na wadda za a yi tare da ragon, da gari na wadda za a yi tare da 'yan raguna kuma, zai zama gwargwadon ƙarfinsa. Zai ba da man zaitun wajen kwalaba shida domin kowace garwa ta garin.
8 Sa'ad da sarki zai shiga, sai ya shiga ta ƙofar shirayin, ya kuma fita ta nan.
9 “Sa'ad da jama'ar ƙasar sun zo yi wa Ubangiji sujada a lokatan ƙayyadaddun idodi, wanda ya shiga ta ƙofar arewa, sai ya fita ta ƙofar kudu. Wanda kuma ya shiga ta ƙofar kudu, sai ya fita ta ƙofar arewa. Kada kowa ya fita ta ƙofar da ya shiga, amma sai kowa ya fita ta akasin ƙofar da ya shiga.
10 Sa'ad da suka shiga, sai sarki ya shiga tare da su, sa'ad da suka fita kuma, sai ya fita.
11 A lokacin idodi da ƙayyadaddun lokatai, gārin hadayar da za a yi tare da bijimi wajen garwa guda ne, haka kuma na wadda za a yi tare da ragon, na wadda za a yi tare da 'yan ragunan kuwa, sai mutum ya kawo gwargwadon ƙarfinsa. A kuma kawo wajen kwalaba shida na man zaitun domin kowace garwa ta gari.