1 Ubangiji ya ce, “Ya kai ɗan mutum, sai ka ɗauki takobi mai kaifi, ka more shi kamar askar wanzami, ka aske kanka da gemunka. Ka auna gashin da ma'auni, don ka raba shi kashi uku.
2 Sai ka ƙone kashi ɗaya da wuta a tsakiyar birnin sa'ad da kwanakin kewaye birnin da yaƙi suka cika. Ka kuma ɗauki sulusi ɗaya ka yanyanka da takobi kewaye da birnin. Sulusi ɗayan kuwa za ka watsar ya bi iska. Ni kuwa zan zare takobi a kansu.
3 Za ka ɗibi gashi kaɗan ka ɗaure a shafin rigarka.
4 Daga cikin gashi kaɗan ɗin nan kuma, sai ka ɗibi waɗansu ka sa a wuta. Daga nan ne wuta za ta tashi a Isra'ila duka.”
5 Ubangiji Allah ya ce, “Wannan ita ce Urushalima. Na kafa ta a tsakiyar al'ummai da ƙasashe kewaye da ita.
6 Ga shi, ta tayar wa ka'idodina da muguwar tayarwa fiye da al'ummai, ta kuma tayar wa dokokina fiye da sauran ƙasashen da suke kewaye da ita. Ta ƙi bin ka'idodina, ta kuma ƙi ta yi tafiya bisa ga dokokina.