11 Allah kuwa ya ce, “Bari ƙasa ta fid da tsire-tsire, na masu ba da tsaba, da itatuwa masu ba da 'ya'ya, kowanne bisa ga nasa iri, waɗanda suke da 'ya'ya masu ƙwaya a cikinsu, waɗanda irinsa suke cikin duniya.” Haka nan kuwa ya kasance.
12 Ƙasa ta fid da tsire-tsire, na masu ba da 'ya'ya waɗanda suke da ƙwayar irinsu a cikinsu, Allah ya ga yana da kyau.
13 Ga maraice, ga safiya, kwana na uku ke nan.
14 Allah kuwa ya ce, “Bari haskoki su kasance a cikin sararin, su raba tsakanin yini da dare, su kuma zama alamu, da yanayi na shekara, da wokatai.
15 Bari kuma su zama haskoki a cikin sarari su haskaka duniya.” Haka nan kuwa ya kasance.
16 Allah kuwa ya yi manyan haskokin nan biyu, haske mafi girma ya mallaki yini, ƙaramin kuwa ya mallaki dare, ya kuma yi taurarin.
17 Allah ya sa su a cikin sarari su haskaka duniya,