1 Waɗannan su ne zuriyar 'ya'yan Nuhu, da Shem, da Ham, da Yafet. Bayan Ruwan Tsufana sai aka haifa musu 'ya'ya.
2 'Ya'yan Yafet ke nan, da Gomer, da Magog, da Madai, da Yawan, da Tubal, da Meshek, da Tiras.
3 'Ya'yan Gomer kuma Ashkenaz, da Rifat, da Togarma.
4 'Ya'yan Yawan kuma Elisha, da Tarshish, da Kittim, da Rodanim.